Abincin gargajiya abinci ne da mutane ke so sosai, amma ba kowa ne yasan salon da za'a bi a sarrafa shi a kicin dinmu na zamani ba. Wannan darasin zai koya maku yanda zaku girka abincin gargajiya kamar su pankaso, miyan taushe, shinkafa da wake, parpesun kayan ciki, paten accha, kunun gyada, lemun tsamiya, zobo da dai sauran su.