Sadarwa a kasuwanci hanya ce ta musayar bayanai tsakanin mutanen da ke saye da sayarwa. Ingantaccen sadarwar kasuwanci shine yanda mai sayarwa zai yi sadarwa tsakaninsa da mai saye har a samu kyakkyawan fahimta. Wannan darasin na ɗauke da cikakkun bayani akan yanda za ku yi sadarwa a harkar kasuwancin ku, fara daga yanda za ku yi bincike a harkar kasuwanci har zuwa yanda za ku kyautata alaka tsakaninku da abokan kasuwanci.